Yayin da yake kara haske game da lamarin kakakin rundunar a jihar Pilato Kaften Salisu Mustafa ya ce ranar ashirin da takwas da daddare suka samu labarin cewa wasu sun kai hari a wasu kauyukan da suka hada da Magama. Ya ce da suka tura dakarunsu zuwa wuraren sai 'yan bindigar suka bude masu wuta lamarin da ya yi sanadiyar kashe mutane ashirin. Ya kara da cewa sun kama wasu daga cikin maharan har da baburan da suka yi anfani da su.
Wasu cikin maharan sun gudu amma sai da suka cinna ma gidajen muaatne wuta. Kakakin sojojin ya tabbatar da cewa sun soma yiwa wadanda suka kama tambayoyi.
Kawo lokacin rahoton nan kura ta lafa an kuma jibge dakaun tsaro da dama. Ana harsashen cewa harin nada nasaba da abun da ya faru makon da ya wuce inda aka kashe shanu da suka ci anfanin gona da aka shuka.
Yanzu dai an tsaurara matakan tsaro a duk fadin jihar Pilato domin shirin ko ta kwana
Zainab Babaji nada karin bayani.