Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Martanin Iyaye Ga Samari Da 'Yan Mata Masu Yiwa Juna Kwace


A yayin da samari da 'yan mata ke tofa albarkacin bakin su musamman kan yadda wasu daga cikin su ke yiwa juna kwace, duk da shike dai dalilan da suka bada basu da nasaba da tarbiyya, dan haka ne masu iya magana suka ce abin da babba ya hango, yaro ko ya taka turmi bazai hango shiba.

Dalilin haka ne muka sami zantawa da wata dattijiya mai suna malama Lubabatu Ibrahim wadda ta yi kira ga matasa samari da 'yan mata harma ga iyaye da su gujewa wannan mummunar dabi'a.

A cewar ta, aboki ko kawa tamkar dan'uwa ne dan haka bai kamata irin haka na fauwa tsakanin su ba, duk wanda yayi hakan tamkar cin amanar aboki ko kawa ne domin kuwa babu abinda ke haifar da wannan in baya ga yaudara da karya.

Dattijiyar ta yi gargadi da bada shawarwari ga iyeye maza da mata, kuma ta yi karin hasken cewa ya kamata iyaye su san samari ko 'yan matan da 'ya'yan su ke hulda da su domin kaucema irin wannan mummunar dabi'a.

Ga cikakkiya hirar..Dandallinvoa.com

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG