Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamfanoni A Najeriya Na Fuskantar Barazanar Durkushewa


Masana'antu
Masana'antu

Kungiyar Kamfanoni A Najeriya (MAN) ta bayyana cewa, tana fuskantar barazanar durkushewa, kasancewa a yanzu haka, kayayyakin da suke sarrafawa a kasar na zamo musu kwantai sakamakon tsadar kayan sarrafawa.

Kungiyar ta koka bisa yadda kudin gudanarwar kamfanonin kasar ya karu da kaso 357.57, sai kuma koma-baya na kaso 1.66 a cinikin kayan da suke sarrafawa.

Kungiyar ta ce yanzu kayayyakin da suke sarrafawa na zamo musu kwantai, saboda babu masaya, ganin cewa irin karin farashi da suka yi wanda ya zamo tilas, saboda karin farashin makamashin wutar lantarki da kaso 200 da gwamnatin tarayya ta yi, sai kuma karanci da kuma tsadar canjin dalar Amurka, hadi da karin kudin ruwa da babban Bankin Najeriya yayi.

MAN, ta ce, a rubu’in farkon shekarar 2024 ta fuskanci kwantan kayayyakin da suka sarrafa da ya haura Naira Triliyan 1.24.

Kazalika, kungiyar ta masu masana’antu ta yi kira yi ga gwamnatin kasar da ta duba lamarin, domin ta haka ne masana’antun zasu iya tsayawa da kafafun su.

A hirarsa da Muryar Amurka Farfesa Hussaini Usman Malami, Masani kuma malami a tsangayar tattalin arziki dake jami’ar Usman Danfodiyo a jihar Sokoto, ya ce dole masana’antu a kasar su shiga irin wannan mayuwacin hali, saboda yanzu tsadar rayuwa ta sa mutane a kasar basa sayen kayayyakin da bai zamo musu tilas ba, Bisa ga cewarsa, karin kudin haraji da gwamnatin kasar ke yi, na mayar da hannun agogo baya, domin masana’antun suna ji a jika.

A nashi bayanin, Hassan Sardauna, daya daga cikin masu sharhi kan lamuran yau da kullum, na ganin wannan barazana da kamfanonin kasar ke fuskanta abu ne da yakamata a dauki mataki tun wuri.

Masana dai na ganin sabbin tsare-tsaren tattalin arziki da gwamnatin tarayya ta zo dashi, danyen ita ce ne mai wahalar lankwasa.

Saurari cikekken rahoton Rukaiya Basha:

Kamfanoni A Najeriya Na Fuskantar Barazanar Durkushewa
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:20 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG