Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

MANARA: Rediyo da Talibijan Akan Tauraon Dan-Adam


Shugaban kungiyar Izalatul Bidi'a Wa Iqamatis Sunnah ta Najeriya (IZALA), Sheikh Abdullahi Bala Lau
Shugaban kungiyar Izalatul Bidi'a Wa Iqamatis Sunnah ta Najeriya (IZALA), Sheikh Abdullahi Bala Lau

Kungiyar IZALA ta kafa gidan rediyo da talibijan akan tauraron dan-Adam da zasu yada wa'azin musulunci da taimakawa alhazai da fadakar da jama'a akan fannoni daban daban

An kaddamar da rediyo da talibijan na Manara ta kungiyar IZALA akan tauraron dan-Adam.

Kaddamarwar ta zo daidai lokacin da Najeriya ke harsashen duk kafafen rediyo da talibijan na kasar su koma kan tauraron dan-Adam cikin wannan watan, wato zasu koma kan naurorin zamani daga na gargajiya da aka saba.

Kafin wannan kaddamarwar da Manara tayi tuni wasu gidajen rediyo da talibijan masu zaman kansu suka koma kan tararon dan-Adam din.

Kamar Manara yawancin gidajen rediyo da talibijan na Hausa dake kan tauraron dan-Adam suna watsa shirye-shiryensu ne daga waje saboda tsaurin dokokin Najeriya na bada lasisin kafasu.

Tashar Manarar da yanzu take yada wa'azin addinin musulunci da wayar da kawunan alhazai kusan su dubu dari da hira kan tattalin arziki da hadin kan al'umma na aiki ne kan tauraron NAISAT karkashin jagorancin kungiyar IZALA.

Gwamna Abdulaziz Yari Abubakar na jihar Zamfara shi yayi jawabin kaddamarwar. Yace zamanin yau na nasara ne kawai domin aikin kafafen labaru. Yace musulunci ya samu nasara ne tare da hanyar yayatawa, wato yin wa'azi. Idan bada wa'azi ba da ba'a samu yaduwar addinin ba.

Shi ma Sultan Abubakar ya bukaci tashar ta fadada ayukanta da yin anfani da harshen turanci domin sako ya samu kabilu a saukake.

Shugaban IZALA Sheikh Abdullahi Bala Lau yace tashar zata hada da na shadantarwa mai ma'ana ta zama kafar yada wa'azi ga miliyoyin mutane a saukake. Yace basu soma karanta labarai ba amma zasu hada shi da shiri domin mata da tattalin arziki da dai sauransu.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:49 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG