Bayanai sun nuna cewa maharani sun yi kwanton bauna ne kan matafiyan a yayin da suke kan hanyar su ta komawa gida daga kasuwar Makera a daren jiya Talata.
Kakakin rundunar tsaro ta special Task Force dake jihar Filato, Capt, Umar Adam, ya tabbatar da afkuwar lamarin kuma yayiwa wakiliyar Sashen Hausa na muryar Amurka Zainab Babaji, karin bayanin cewa baya ga mutane Takwas da suka rasa rayukan su, jami’an sun garzaya asibi ta wasu hudu da suka jikkata.
Ya kuma kara da cewa a lokuta da dama ana samun bata-gari wadanda ke sa kayan sarki dauke da makamai domin aikata mummunar barna irin wannan. Capt Umar ya bayyana cewa Kawo yanzu, akwai jami’ai na musamman dake sintiri a yankin.
Wani daga cikin wadanda suka ganewa idanun su, Mr John Daliop Haruna, ya bayyana wa Zainab Babaji, cewa a dai-dai lokacin da suke zantawa da ita ya ganewa idanunsa gawawwakin matasa guda Tara a kwance, yayin da wasu kuma ke karbar magani a asibiti.
Daga yankin Awe, duk a jihar Nasawa, an sami asarar rayuka a wata arangama da aka yi tsakanin makiyaya da manoma kamar yadda shugaban kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders, Alhaji Muhammed Hussaini ya bayyana.
Domin karin bayani, saurari rahoton Zainab Babaji daga jihar Filato.
Facebook Forum