Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnan Anambra Ya Kori Wasu Domin Jam'iyyar Adawa


 JAM'IYYAR APGA
JAM'IYYAR APGA

Gwannan jihar shine Uban jihar kuma ko ana sonsa ko ba’a sonsa yakamata ya nuna dattako ya tabbatar kowa ya samu damar lasar romon dimokradiya.

Ana zargin gwamna Wille Obiano na jihar Anambra da korar jami’an gwamnati dake goyon bayan jam’iyyun adawa a zaben Gwamna na ranar 18, ga wannan watan, a yayinda wadanda korar ta shafa na cewa hakkin sune su zabi duk wanda suke so.

Cif Igbo Kwubiri,mataimakin babban darakatan kungiyar “Godwin Ezemo campaign organization” na daya daga cikin wadanda batun ya shafa, yace Gwamna ya kore shi ne domin yana goyon bayan Ezemo, dan datakarar jam’iyyar EPA, baya, Ya kara da cewa Gwamnan yace masa ya kasance a jam’iyyar APGA, amma sai yaga cewa ana so a maida shi bawa ne a jam’iyyar ta APGA.

Igbo Kwubiri, yace bas hi kadai aka kora ba suna da yawa alal misali Augustine Ejubendu, Ifeanyi Ezedum, da kuma wasu da Gwamnan ya kora.

Mr. Ogochukwu Ogbonnaya, wani mai sharhi kan lamuran yau da kullum, yace babu wani shugaba a duk fadin duniya da zai so yana mulki ana yi masa rashin kunya saboda haka Gwamnan nada ikon ya tsigesu daga mukamansu muddin ya tabbatar suna yi masa rashin kunya.

A nasa ra’ayin wani dalibi mai suna Promise Ude, yace ba abun mamaki bane saboda wannan ba shine na farko ba a kasar kuma yana daya daga ciki abubuwan dake zubar da mutuncin siyasar nahiyar Afirka.

Gwannan jihar shine Uban jihar kuma ko ana sonsa ko ba’a sonsa yakamata ya nuna dattako ya tabbatar kowa ya samu damar lasar romon dimokradiya.

Wakilin muryar Amurka Alphonsus Okoroigwe, yayi kokarin kakakin gwamna da kuma kwamisinan watsa labarai na jihar amma abin ya chi tura.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:12 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG