Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Marayu Sun Samu Tallafi a Jihar Neja


Dr. Babangida Aliyu Gwamnan Jihar Neja.
Dr. Babangida Aliyu Gwamnan Jihar Neja.

Sama da marayu dari hudu da hamsin suka samu tallafin kayan sallah a jihar Neja.

Marayun da suka samu tallafin sun fito ne daga garuruwan Minna, Bidda da kuma karamar hukumar Kontagora.

Tallafin ya fito ne daga wata gidauniya mai suna Rahama Foundation da gwamnatin jihar Neja da kuma kungiyar IZALA mai gabatar da wa'azin addinin Musulunci a Najeriya

Dr. Muhammed Sani Ashir na jami'ar Bayero dake Kano da kungiyar IZALA ta turo jihar Neja domin gabatar da wa'azin Ramadan yayi karin haske akan dalilinsu na tallafawa marayun. Yace idan an barsu ba'a kula da rayuwarsu ba ta fuskar suturarsu da abincinsu da iliminsu to za'a samu matsala dasu nan gaba. Idan sun girma ba tarbiya to an shiga wahala ke nan. Suna iya zama 'yan daba ko barayi ko 'yan ta'ada. Yakamata a kula dasu su ma su rayu kamar yadda kowa ke rayuwa.

Malam Awal Kiki mataimakin sakataren tantance marayun a Kontagora ya bayyana yadda suka zakulo marayun da aka tallafawa. Bisa ga hadin kan malamai da kwamitin da aka kafa aka zakuo marayun.

Marayun da suka samu tallafin sun bayyana jin dadinsu.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:55 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG