Kwamitin tallafawa mutanen da suka hadu da bala'o'in ambaliyar ruwa, da na Boko Haram da kuma sauran tashe-tashen hankula irin na kabilanci da na addini ya isa jahar Bauchi.
Kwamitin ya gana da jami'an gwamnati, da shugabannin al'umma, sannan ya rarraba kayan agaji ga 'yan gudun hijira.
Wazirin Katsina, Dakta Sani Sani Abubakar Lugga shi ya jagoranci tawagar kwamitin zuwa garin Bauchi;
Wata mata 'yar gudun hijira ta ce garin gudun ceton rai aka harbe ma ta maigidan ta aka kashe shi. Ta ce ba su da komi, an kona mu su duk abun da suka mallaka. Sannan ta yi godiya ta ce tallafin da aka ba su zai taimaka mu su sosai.
Wakilin Sashen Hausa a jahar Bauchi, Abdulwahab Mohammed ne ya aiko da rahoton.