Marayun sun samu tallafin tufafin salla da kayan abinci na kwamitin tallafawa marayu na kungiyar IZALA a jihar Sokoto albarkacin watan Ramadana.
Kwamitin marayun ya tattara kayan tallafin ne daga sadakoki da daidaikun jama'ar musulmi da wadanda hukumomi ke bayarwa cikinsu har da Sarkin Musulmi wanda ya bayar da turamen atamfa har dari uku ga asusun.
Ambasado Abubakar Shehu Wurno shi ne shugaban kwamitin na tallafawa marayun a jihar Sokoto. Banda bayar da sutura da abinci Shehu Wurno yace nan gaba zasu taimaka a wani bangare daban. Zasu tantance marayu zasu kuma taimaka masu ta wajen ilimi na addini da na zamani tun daga firamare har zuwa sakandare.
Sheikh Muhammed Haruna Gombe wanda kungiyar IZALA ta tura Sokoto domin yin tafsirin azumin bana shi ne ya soma assasa asusun na tallafawa marayu farkon zuwansa Sokoto a shekarar 2009 kafin shugaban IZALA na kasa ya mayar da tallafin na kasa baki daya.
Taimakawa marayu, zaurawa da nakasassu yana da anfani a Musulunci. Jama'a su tashi su taimaki marayu su jidadi kamar wadanda suke da iyaye domin Allah Ya ji tausayinsu ranar da suka mutu.
Ga rahoton Murtala Faruk Sanyinna.