Kungiyar Tarayyar Turai da ake kira EU a takaice tare da hukumar raya al'adu ta Burtaniya wato British Council, sun yi wani taron bita don shugabanni da masu ruwa da tsaki a yankunan Najeriya da rikicin 'yan kungiyar Boko Haram ya shafa, musamman a arewa maso gabashin kasar.
Wanann taron da aka yi a jihar Adamawa, na daya daga cikin tarukan da aka shirya a jihohin da rikicin ‘yan kungiyar Boko Haram ya shafa. Masana da suka halarci taron sun yi kira ga jama’ar da abin ya shafa da su kai zuciya nesa.
Wakiliyar gwamnan jihar Adamawa a wurin taron Mrs. Rhoda Zira, ta ce ta’addanci ba shi da kabila ko addini don haka ya kamata a daina nuna wa juna yatsa a kuma kawar da zargi a tsakanin jama’ar da matsalar ta shafa.
A lokacin da yake bayani, Abdulkadir Bello Ahmad, wanda shine jagoran shirin wanzar da zaman lafiya na hukumar raya al'adu ta Burtaniya, da ake wa lakabi da MCN, wato Managing Conflicts In North East, Nigeria, ya bayyana nasarar wannan aiki na sulhunta jama’a da suke yi yanzu.
Mallam Yakubu Musa, dake zama a daya daga cikin yankunan da rikicin Boko Haram ya shafa ya ce, taron yana da muhimmanci musamman ga matasa, domin ana zaburar da su game da samun aikin yi maimakon zaman banza.
A saurari rahoton cikin sauti daga Jihar Adamawa a Najeriya.
Facebook Forum