A cigaba da jin ra’ayoyin ‘yan Najeriya da ake yi game da makomar kasar da kuma kundin tsarin mulkin kasar, Majalisar Dokokin Jahar Naija ta yi zaman sauraren ‘yan kasa a Ginin Majalisar.
Shugaban Majalisar Dokokin jahar ta Naija Ahmed Marafa Guni ya yi bayani a wurin taron jin ra’ayin cewa Majalisar Dokokin Tarayyar Najeriya ce ta bayar da umurnin a yi wannan zaman saboda ‘yan kasa su san halin da ake ciki da kuma inda aka dosa game da tanaje-tanaje wajen 15 da ake son a sake dubawa; wadanda su ka hada da batun rage shekarun matasan da za su iya shiga takarar siyasa daga shekaru 30 zuwa ashirin da biyar; da tsananta hukunci kan masu laifin fade; da batun baiwa kananan hukumomi ‘yancin cin gashin kansu da dai sauransu.
Wani da ya halarci taron, wanda kuma shi ne shugaban kungiyar shugabannin kananan hukumomin Najeriya Honorabul Gambo Tanko ya ce muddun kudin kananan hukumomi su ka je asusun kananan hukumomi kai tsaye a maimakon bin ta wata kafa, to za a iya irin aikin da jama’a ke bukata kai tsaye. Shi kuma shugaban jam’iyyar adawa ta APGA a jahar Musa Aliyu Liman ya ce taron bai da wani amfani saboda ba a cika amfani da shawarar jama’a ba. Honorabul Bello Agwara ya ce za a tura ma Majalisar Dokokin kasa ra’ayoyin da aka tattara.
Ga Mustapha Nasiru Batsari da cikakken rahoton:
Facebook Forum