Manchester City ta nuna sha’awar sayen dan wasan Juventus Cristiano Ronaldo kamar yadda jaridar Sky Italiya ta ruwaito.
Kungiyar ta City ta yi wa Ronaldo tayin kwatiragin shekara biyu akan kudi euro miliyan 15 a cewar rahotanni.
Sai dai Juventus ta ce ba za ta sayar da dan wasan akan wannan farashi ba sai dai euro miliyan 25
An yi ta yayata cewa Ronaldo, dan shekara 36, wanda ya zura kwallaye 118 a wasannin 292 a lokacin yana kungiyar Manchester United a tsakanin shekarun 2003 zuwa 2009, na da burin barin kungiyar amma Juventus tana fatan dan wasan ya zauna.
Shi dai Ronaldo bai tuntunbi kungiyar ta Juventus kai-tsaye ba, kan cewa yana so ya tafi.
Kwantiraginsa da Juventus zai kare ne a watan Yunin 2022.
City, ita ce kungiya kadai da take zawarcin Ronaldo dan asalin kasar Portugal.
Rahotanni sun ce City ta koma neman sayen Ronaldo ne bayan da ta gaza sayen dan wasan Tottenham Harry Kane.
Kungiyar ta Pep Guardialo ta yi ta zawarcin kyaftin din Ingilan wanda aka masa kudi euro miliyan 150, amma dan wasan gaban ya yi kememe ya ce zai zauna a Tottenham.