A yayin da ake shirye shiryen rantsar da sabuwar gwamnatin da ta lashe babban zabe a Najeria, da alama malaman makaranta zasu sami nasu rabon a wannan sabuwar demokaradiyya kamar yadda jama'a da dama ke hangen samun wani dgagarumin canji a kasar.
Wakilin sashin Hausa Hassan Maina Kaina a hirarsa da Comrade Ibrahim Lawal dan kwamitin zartaswa na kungiyar malamai ta kasa wanda kuma shine shugaban kungiyar a jahar Yobe yayi wani karin haske da bayyana cewa;
“Tunb a yau ba mundada muna jiran wannan shiri na tandawa malaman makaranta gidaje, ko a jahohinmu mundade muna wannan fafutuka domin yawancin malamai basu da gidaje. Dan haka yin wannan lallai abin farin ciki ne ga dukkan malaman Najeriya bakidaya.”
A ra’ayin wani malamin makaranta mai suna Baba Adamu Idi kuma, cewa yayi an dade ana yi masu alkawura kamar haka amma har yanzu basu gani a kasa ba, kuma ya kara da cewar suna sa ran wannan sabuwar gwamnati zata dubesu da idon rahama.
Bayan haka kuma, yayi kira ga gwamnati da ta sake shirin horar da malaman domin samun Karin ingancin ilimi a Najeriya baki daya domin a ganinsa wannan wajibi ne domin rashin sanin aikin malami shine makasudin raguwar martabar ilimi a kasar.