Ranar bakwai ga watan Afirilu na shekarar 2011 Mahamadou Issoufou ya dare kan karagar mulkin kasar Jamhuriyar Nijar, wato yau ya cika shekaru hudu ke nan yana shugabancin kasa dake makwaftaka da wasu kasashen yammacin Afirka da suka hada da Najeriya.
Yayin tunawa da cika shekaru hudu da zama shugaban kasa Mahamadou Issoufou ya amsa tambayoyi daban daban daga 'yan jarida domin sanin inda kasar take yanzu.
A karkashin shugaban aka yi tsarin 'yan Nijar su ciyar da 'yan Nijar, wato tsarin inganta noman cimaka. Akwai kuma tsarin gina layin dogo domin inganta harkokin sufuri a kasar. Ya kuma samar ma matasa guraban aiki.
Akan irin cigaban da kasar ta samu a karkashin shugabancin Issoufou Malam Sule Audu na kungiyar ma'aikata yace a fannin zaman lafiya an samu cigaba sosai. Yace gwamnati ta sa kudi sosai domin biyan jami'an tsaro da samar masu kayan aiki ingantattu da zasu sa su yi maganin duk wata matsala da ka kunno kai. Yace akwai matsalar Boko Haram a Difa akwai kuma a Mali makwafciyarta. Sojojin kasar sun fuskanci duk matsalolin ba tare da karaya ba. Ya cigaba da cewa yau a Nijar an yi gine-ginen hanyoyi, makarantu, asibitoci da wasu makamantansu. Gwamnatin tayi abubuwan dake taimakawa rayuwar jama'a. An dauki ma'aikata sosai an kuma kara masu albashi.
A fannin siyasa da fadin albarkacin baki babu wanda ake kutuntawa. Ba'a takura kowa ba ba'a kuma takurawa 'yan jarida ba. Babu wani rikicin siyasa da ya dakatar da aikin gwamnati.
To saidai duk kokarin samun albarkacin bakin 'yan adawa ya cutura. Kowa aka tuntuba sai ya ce zai kira amma kuma ba zai kira ba. Babu wani dan adawa da ya yadda ya tofa albarkacin bakinsa akan ayyukan gwamnatin Mahamadou Issoufou.
To saida wani Malam Abdulrahaman Kuli malamin makaranta yace a fuskar siyasa akwai matsaloli saboda akwai rashin jituwa tsakanin masu iko da 'yan adawa..
G arohoton Shaaibu Mani.