Bayan tafka mahawwara Majalisar ta kwaskware ayar doka ta farko ta kundin tsarin mulkin kasa wace ke bayani kan taken Nijer. Daukacin ‘ayan majalisa 149 da suka halarci zaman ne suka yi na’am da gyaran fuskar abinda ke nufin wakilan al’ummar ta Nijer sun amince da sabon samfarin taken na kasa mai sunan L’honneur de la Patire wato mutuncin kasa.
Ministan al’adu Mohamed Hamid ya yaba da hadin kan ‘yan majalisar suka bai wa gwamnati a sabuwar tafiyar ta sa gaba.
Koda yake sun kada kuria’r amincewa da sabon taken na kasa ‘yan adawa a ta bakin dan Majalisa Souamana Sanda na cewa ba shi ne abinda ke gaban talakawan Nijer ba a yau idan aka yi la'akari da tarin matsalolin da ake fuskanta a fannoni da dama.
A nan gaba kadan shugaban kasa Mohamed Bazoum zai saka hannu kan takardar da za ta soke tsohon taken La Nigerienne don kaddamar da sabon taken da aka yi wa suna l’honneur de la Patrie.
Saurari rahoton cikin sauti: