Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Kan Kan Kan Tsakanin Tarayya Da Lumana A Zaben Mazauna Ketare


CENI
CENI

Sakamakon wucin gadin na zaben da aka gudanar a ranar 18 ga watan yunin 2023 da nufin aika wakilan mazauna ketare (‘yan Diasfora) a majalissar dokokin Nijar na nuna an yi kan-kan-kan a tsakanin PNDS Tarayya madugar jam’iyyun da ke mulki da jam’iyyar Moden lumana ta ‘yan adawa.

‘Yan Nijer mazauna kasashen waje kimanin 103164 daga cikin 205314 da suka yi rajista ne suka halarci runhuna a zaben 18 ga watan Yunin 2023 da nufin tantance mutanen da za su wakilce su a majalisar dokokin kasa inji shugaban hukumar zabe ta CENI a yayin kwarya kwaryan bukin da aka shirya a wannan Laraba a dakin taro na 'Palais des Congres' da ke birnin Yamai.

Me Issaka Sounna ya kara da cewa daga cikin kujeru 5 da aka yi zawarcinsu jam’iyyar MNSD NASARA ta sami kujera 1 sannan PNDS TARAYYA ta lashe kujeru 2, sai kuma MODEN LUMANA wadda ta sami kujeru 2.

Jam’iyyar MODEN LUMANA wace ta fafata a zaben na 18 ga watan Yuni cikin yanayin rarrabuwar kawuna na alfahari da yadda ‘ya'yanta suka jajirce har aka kai ga samun abin da wani kusanta Mahamadou Maidouka ke kira galaba.

A shekarar 2016 ne ‘yan Nijar mazauna ketare suka fara aiko da wakilai a majalissar dokokin kasa, a wancan lokaci daga cikin kujeru 5 PNDS TARAYYA na da 3. Ganin yadda a wannan karon ta tashi da kujeru 2, wasu na ganin abin tamkar wata manuniya ce ga jam’iyyar mai mulki. To amma Boubacar Sabo na alakanta lamarin da tsarin fasalin zabe.

Jam’iyyu 10 ne suka fafata a wannan zabe da ke matsayin na cike gurbin kujeru 5 na majalisar dokokin kasar mai kujeru 171 a bisa ka’ida ‘yan Nijar mazauna ketare kan kada kuri’unsu ne lokaci guda da sauran jama’ar cikin gida. To sai dai annobar coronar da aka fuskanta a 2020 ta tilasta dage zaben na ‘yan diasfora. Yanzu dai kallo ya koma wajen kotun tsarin mulkin kasa wace ke da hurumin tabbatar da sahihancin sakamakon zaben wato ko ta yi na’am da shi ko akasin haka.

Saurari rahoton cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:17 0:00

Zaben 2023

TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Tasirin Da Zaben Donald Trump Zai Yi A Harkokin Kasashen Duniya.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:50 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG