Anan Amirka mutum yana iya cika motarsa samfurin jib da mai idan yana da dala saba’in da biyar, ko kuma ya kai iyalinsa liyafar cin abincin dare. To amma a wani kauyen Afrika dala saba’in da biyar din yana iya fitar da kauyen kacokan dinsa daga kangin fatara da talauci.
Dala saba’in da biyar ya ishe wani mazaunin kauye a Nigeria jari. Chiris Egbulen shugaban wata kungiyar aikin sa kai da ake kira Africa Action shi yayi wannan furucin. Harma ya bada misali da wata mace wadda aka baiwa dala saba’in da biyar, ta yi amfani da kudin ta zuba jari harma ta dauki mutane biyu aiki suna taimakon ta.
Shi dai Chris Egbulen a Nigeria ya girma. Amma ya dade yana koyarwa a wata Makarantar dake jihar Luisiana nan Amirka. To amma yanzu yana maida hankali ne akan yadda zai taimaki mutane su fita daga kangin fatara da talauci.
Kungiyar daya kafa, mai suna Africa Action tafi maida hankali wajen taimako mazauna kauyukn Nigeria, kasar data fi kowace kasa a Nahiyar Afrika yawan yawan jama’a da kuma kasar Saliyo daya daga cikin kasashen duniya da suka fi kowace kasa talauci.
Facebook Forum