Sakamakon gabatar da wani kudiri mai matukar mahimmanci ga kasa da dan majalisa, Oboku Oforiji ya yi, a jiya talata Majalisar Wakilan Najeriya ta bukaci a dakatar da karin kaso 50 cikin 100 na kudin kiran waya da sayen data nan take.
Majalisar ta kuma koka da rashin ingancin ayyukan kamfanonin sadarwa inda ta jaddada cewar bai kamata su yi karin kudin kiran waya da sayen data ba har sai sun inganta ayyukansu.
‘Yan majalisar sun kuma umarci hukumar NCC, mai kula da kamfanonin sadarwar Najeriya da ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Bosun Tijani, dasu dakatar da karin harajin saboda halin matsin tattalin arzikin da ake fama da shi a kasar.
Hakan na zuwa bayan da kamfanonin sadarwar kasar suka fara aiwatar da sabon tsarin harajin da hukumar NCC ta amince da shi tunda fari.
Masu amfani da shafukan sada zumuntar da suka yi amfani da ayyukan kamfanonin sadarwar a jiya Talata sun lura da karin kaso 50 cikin 100 kan kudaden kiran waya da sayen data da kuma aikewa da sakon kar ta kwana.
Dandalin Mu Tattauna