Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gbajabiamila Ya Musanta Zargin Warewa Ofishinsa Nb20 A Kasafin Kudin Shekara Ta 2024


Shugaban Ma'aikatan Fadar Shugaban Najeriya Femi Gbajabiamila
Shugaban Ma'aikatan Fadar Shugaban Najeriya Femi Gbajabiamila

Shugaban Ma'aikata a fadar shugaban kasa Femi Gbajabiamila, a wata sanarwa da ya wallafa a kafar sadarwa ta X (twitter) a hukumance, ya karyata labaran da ake yadawa a kafafen sada zumunta na yanar gizo kan makudan kudaden da ake zargin an ware wa ofishinsa a kasafin kudi.

A ranar Laraba, 06 ga Disamba, 2023 ne shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Femi Gbajabiamila, ya fitar da wata sanarwa a hukumance a matsayin martani ga rahotannin da ke nuni da cewa an ware masa wani babban kaso a kasafin kudin shekarar 2024 don gyara gidansa na kashin kansa.

Da yake mai da martani kan labarin da ya karade kafar yanar gizo, musamman wadanda ke nuna kasafin Naira biliyan 10 na gyaran gidansa da kuma karin Naira biliyan 10.1 na manhajar kwamfuta, Gbajabiamila ya jaddada rashin ingancin labarin tare da yin watsi da illahirin bayanan da labarin ya kunsa na ikirarin kudin da aka ware ma ofishinsa a kasafin shekarar 2024,

Ya nanata cewa a yanzu haka yana aiki ne daga gidansa na kashin kansa ba na gwamnati ba.

A wata sanarwa da aka wallafa a shafinsa na X (twitter) a hukumance, Gbajabiamila ya tabbatar da cewa an ware kasafin kudin ne domin gyaran sashin fadar shugaban kasa da ke barikin soji na Dodan Barrack da kuma masaukin mataimakin shugaban kasa da ke Legas.

Ya kara da cewa, "kudade da masu bayyana ra'ayi na yanar gizo da masu yada labaran karya suka yi, maganar gaskiya itace an tanadi kudaden ne don gyara sashen fadar shugaban kasa da ke barikin soji na Dodan Barrack da kuma Gidan Mataimakin Shugaban Kasa a Legas."

Bugu da kari, Gbajabiamila ya bayyana cewa wadannan kudade sun kunshi tsare-tsare da nufin sabunta hanyoyin sarrafa bayanai da sadarwa a cikin fadar shugaban kasa, tare da daidaita su bisa tsari da ka'idoji irin na zamani, da samar da ababen hawa ga ma'aikatan fadar shugaban kasa.

Tsohon kakakin majalisar wakilan ya kuma jaddada mahimmancin samar da sahihan bayanai wajen wanzar da kyakkyawar muhawarar jama'a game da ayyukan gwamnati.

Gbajabiamila ya sake nanata kudurin gwamnatin na tabbatar da gaskiya, yana mai cewa, "Wannan gwamnati tana maraba da kuma karfafa bin diddigin abubuwan da gwamnati ke kashewa; wannan ne ya sa gwamnati ta fitar da bayanai game da kasafin kudi a bainar jama'a."

A ƙarshe, ya roki masu irin wannan halayya ta yada labarai, da su fahimci irin alhakin da maganganunsu ke dauke da shi, yana mai jaddada muhimmancin kafa hujjojin da ake iya tabbatarwa maimakon batanci da karya maras tushe.

Har yanzu dai masu bin diddigi da manazarta na ci gaba da nazarin kasafin kudin shekara ta 2024 da shugaban kasa ya mikawa majalisar dokoki, inda ake ta samun mabanbantan ra'ayoyi da soke-soke game da yadda kasafin kudin ya bayyana.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG