Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Umarci INEC Ta Mika Takardar Shaidar Cin Zabe Ga Wasu Jam'iyyu


Shugaban hukumar INEC a Najeriya, Prof. Mahmoud Yakubu
Shugaban hukumar INEC a Najeriya, Prof. Mahmoud Yakubu

A Najeriya babbar kotun tarayya da ke Abuja karkashin mai shara’a Bello Kawu, ta umarci hukumar zabe mai zaman kanta INEC da ta mika takardar shaidar nasarar cin zaben da ya gudana a wannan shekarar ga 'yan takarar jam’iyyun PDP, PRP da kuma NNPP, a jihar Bauchi.

Kafin hukuncin kotun kuwa, hukumar zaben ta INEC ta ba da takardun shaidar nasarar zaben ne ga 'yan takarar jam’iyyar APC.

Mazabun da hukuncin kotun ya shafa sune mazabar sanatan Bauchi ta kudu, da na dan majalisar tarayya na Zaki, da na dan majalisar tarayya na Alkaleri, da na majalisar tarayya na Darazo/Ganjuwa, sai kuma na majalisar tarayya na Gamawa.

Jam’iyyar PDP tana da kujeru guda uku da suka hada da na sanata, da kuma 'yan majalisar tarayya guda biyu.

Saurari rahoton Abdulwahab Muhammad daga Bauchi domin jin cikakken bayani:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:33 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG