A kowacce shekara gwamnatin tarayyar Najeriya, jihohi da kananan hukumomi na gabatar da kasafin kudinsu bayan ‘yan majalisu sun tafka mahawara mai zafi, yayin da al’ummar da ake yi dominsu ke fatan ganin sauye-sauye a fannoni dabam-daban.
A kokarinta na daukar matakan dakile cutar coronavirus wadda ke shafar numfashin bil’adama, gwamnatin tarayyar Najeriya na shirin rage naira tiriliyon daya da digo biyar daga kasafin kudin shekarar nan ta 2020. Wannan kuma na zuwa ne bayan da farashin mai ya fadi a kasashen duniya.
Ko da yake, wasu 'yan kasar na cewa talakawa basu ganin ayyukan da ake yi don moriyarsu.
Masanin harkokin tattalin arziki Mr. Kicime Gwatau, ya jinjina wa gwamnatin Najeriya saboda kokarin da take yi, musamman matakin da ta dauka na rage farashin man fetur a kasar a daidai lokacin da ake fama da barazar cutar coronavirus.
Malam Umar Faruk Musa, wani mazaunin birnin Jos ne, ya ce kowacce shekara suna jin hukumomi na karanta kasafin kudi na makudan kudade a kafafen yada labarai amma talakawa ba su gani a kasa.
Wata ma’aikaciyar gwamnatin Najeriya da ta bukaci a sakaya sunanta, ta ce rashin bayanai daga bangaren hukumomin kasar akan yadda ake aiwatar da kasafin kudin na barin talakawa da sauran al’umma cikin duhu akan ayyukan gwamnati.
Shi kuma wani dan jarida a jihar Filato, Wika Gofwen, ya ce zasu taimaka wajen samar da bayanai ta yadda 'yan kasa zasu fahimci yadda gwamnati ke aiwatar da ayyuka dominsu.
Ga karin bayani cikin sauti.