Tun da aka kirkiro jihar, al'umma basu taba biyan gwamnati kudin ruwan da suke sha ba. A kudurin da majalisar ta fito da shi, kungiyoyi masu zaman kansu, yan kasuwa da ma wasu na iya shiga harkar samarda ruwa na sayarwa al'umma. Majalisar ta ce gwamnati kadai ba zata iya samar wa al'ummarta ruwa ba.
To amma wasu masana sun ce akwai kuskure a shirin domin ruwa ko ina yake malakar gwamnatin tararya ne kamar yadda yake a kundin tsarin mulkin kasar. Kamata yayi majalisar ta fara da gwamnatin tararya domin samun hanyar cimma manufarta.