Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gangamin Jam'iyyar ACN a Legas


Hoton Nuhu Ribadu dan takarar jam'iyyar ACN a zaben 2011.
Hoton Nuhu Ribadu dan takarar jam'iyyar ACN a zaben 2011.

Jam'iyyar ACN ta yi babban taro a Legas inda ta rushe kanta domin hadewa da sauran jami'un hamayya

A cigaban shirinta na hadewa da sauran jam'iyyun hamayya, yau ACN ta yi babban gangami a Legas wanda ya tattaro manyan yan jamiyyar daga sassa daban-daban a Najeriya. Mutane da suka halarci taron sun hada da tsofofin gwamnoni kamar su Alhaji Lateef Jakande da ma shugaban CPC General Mohammed Buhari.

Lokacin taron shugabanninta sun nemi izinin membobi su rushe jam'iyyar domin su hade da sauran yan hamayya a kafa sabuwar jam'iyyar APC. Mambobi sun nuna amincewarsu daga hannuwansu.

Yayin da yake jawabi Alhaji Jakande yace hadewarsu ita ce hanaya kadai da za'a iya kada PDP wadda ya kira jam'iyyar barayi. Shi ma Genral Buhari ya yi jawabi ya kuma yarda da kalamun Alhaji Jakande.

Daga yanzu dai babu jam'iyyar ACN a hukumance. Mambobi sun sa ido suna jiran INEC ta yi masu ragistar APC.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:37 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG