A zaman da Majalisar ta yi a jiya Laraba, karkashin jagorancin shugabanta Kabiru Alasan Rurum. ‘Yan Majalisar sun yi muhawara akan kudurin da aka gabatar game da batun bincikar Mai Martaba Sarkin Kano da masarautarsa.
Majalisar dai na tuhumar mai martaba Sarkin Kano, Mallam Mohammadu Sanusi II, da aikata ba dai-dai ba akan abubuwa guda takwas. A cewar ‘dan Majalisa Ibrahim Ahmed Gama, akwai korafi game da yadda Sarki ke tsoma kansa cikin harkokin siyasa, sai kuma bayanai da aka samu kan yadda masarautar ta sarrafa makudan kudade ba bisa ka’ida ba.
Dokar da ta kafa masarautar Kano ta bayyana cewa masarauta ba zata kashe sisin kwabo ba, har sai ta kaiwa Majalisar Dokokin jihar Kano ta duba ta amince. Sai dai Ibrahim Gama, ya ce tun hawan mai martaba Sarkin Kano bai taba kaiwa Majalisar ba domin a amince masa kashe kudade.
Wannan kwamiti dai da Majalisar ta baiwa makonni biyu domin ya kammala bincikensa kuma ya gabatar da rahoto, yana karkashin jagorancin mai tsawatarwa ne a zauren Majalisar, Labaran Abdul.
‘Daya daga cikin ‘yan kwamitin Baffa Babba ‘Dan Agundi, yace zasu gayyato wanda ya mika korafin domin ‘kara bayani gaban kwamitin, haka kuma za a gayyato mai martaba Sarkin Kano da duk wadanda abin ya shafa domin su bada na su bahasin.
Wannan batu dai na zuwa ne ‘kasa da makonni biyu bayan da hukumar yaki da rashawa ta jihar Kano, ta kaddamar da na ta binciken akan Mai Martaba Sarki da Majalisar masarautarsa game da wannan batu na kashe kimanin Naira Biliyan shida cikin shekaru uku da suka gabata ba bisa ka’ida ba.
Domin karin bayani saurari rahotan Mahmud Ibrahim Kwari.
Facebook Forum