Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kubutar da 'Yan Matan Chibok 82 Soma Tabi Ne - Gwamnatin Tarayya


Shugaban Tarayyar Najeriya Muhammad Buhari
Shugaban Tarayyar Najeriya Muhammad Buhari

Gwamnatin tarayyar Najeriya tace zata dukufa wajen tabbatar da an sako sauran 'yan matan Chibok da duk wasu 'yan kasar dake hannun Boko Haram bayan da aka samu kubutar da 'yan matan 82.

Malam Garba Shehu kakakin fadar gwamnatin tarayya yace lallai sako 'yan matan 82 soma tabi ne saboda gwamnatin da shugaba Buhari ke jagoranta ta dukufa wajen ganin an sako sauran 'yan matan da kungiyar Boko Haram ke rike dasu ta daukan matakan da suka dace.

Dangane da yadda aka samu har aka kubutar da 'yan matan, Malam Garba Shehu yace tattaunawa ce aka yi. Yace su 21 da aka fara samu daga bakinsu aka ji labarin cewa akwai wasu guda 83 a wuri kaza da suka ambata.

Masu shiga tsakani su ne suka tambayi kungiyar game da su 83 din kuma suka tabbatar suna hannunsu. Malam Garba yace an yi wata da watanni ana tattaunawa tare da hadin kan kungiyoyin cikin gida da na waje. Da suka yadda zasu sakesu daya daga cikinsu tace ita ta samu miji ba zata dawo ba.Dalili ke nan da aka samu 82 maimakon 83 din.

Ita ma gwamnati ta bada 'yan kungiyar guda biyar da take tsare dasu. Su ne aka yi musaya dasu kafin a sako 'yan matan 82.

Akan sukar da wasu 'yan kasa keyi na cewa ta yaya za'a saki mugayen mutanen da suka haddasa barna cikin kasar, sai Malam Garba yace duk wanda yayi wannan maganar watakila ba zai sa kansa a irin halin da iyayen yaran suke ciki ba ke nan.Yace wanda yake maganar idan da akwai diyarsa cikinsu ba zai yi irin wannan maganar ba.

Malam Garba ya cigaba da cewa duk duniya ana yin irin wannan musayar. Yayi misali da kasar Israila wadda take yaki da 'yan ta'addan Falesdinu amma tana musayar fursinoni da kungiyar domin karbar gawarwakin nata mutanen ma. Yace akan gawar soja guda sai da Israila ta saki fursinoni fiye da dubu biyu. Yace a Najeriya gwamnati tana da 'yan Boko Haram dubbai da take tsare dasu, saboda haka idan an saki biyar me aka yi.

Inji Malam Garba an riga an cigaba da yakin da ake yi dasu. Kuma yanzu kala ake yi domin a kammla yakin. Sakar masu mayaka biyar ba zai canza komi ba, injishi. Yace saboda haka kada mutane su damu da sakin mayakan.

Akwai tabbacin sauran 'yan matan za'a bukutar dasu ta hanyar tattaunawa da wasu hanyoyin. Yace baicin kokarin kwato mutanen dake hannun 'yan ta'addan ana neman yadda za'a samu zaman lafiya kuma akwai 'yan Najeriya da dama da suke ba gwamnati shawarwari akan lamarin.

Ga rahoton Umar Faruk Musa da karin bayani

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG