Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Jihar Filato Ta Sake Jaddada Dokar Hana Tuka Baburan Okada cikin Birnin Jos


Gwamnan Jihar Filato Barrister Simon Bako Lalong
Gwamnan Jihar Filato Barrister Simon Bako Lalong

Biyo bayan wata hatsaniya tsakanin masu tuka babura, da ake kira okada, da 'yansanda a birnin Jos wanda yayi sanadiyar mutuwar mutum daya, gwamnatin jihar ta sake jaddada dokar hana tuka babura a birnin.

Hatsaniyar ta auku ne jiya da safe yayinda 'yansanda ke kokarin aiwatar da dokar hana tuka babura cikin birnin Jos, har ma suka yi anfani da barkonon tsohuwa domin tarwatsa masu baburan

Mai baiwa gwamnan jihar Filato shawara akan.harkokin labarai Emmanuel Nanly yace gwamnati ta kara jaddada dokar hana tuka baburan ne don kaucewa abun da iya faruwa. Har yanzu takunkumin da gwamnati ta sawa baburan sana'ar Okada ko Going yana nan ba'a kawar da shi ba.

A cewarsa mutanen ne suka taru suna kushewa dokar tare da nacewa si sun cigaba da sana'ar Okada din cikin birnin da doka ta haramta. Yace akan wannan batun gwamnati ta tsaya tsayin daka sai dokar tayi aikinta.

Wani Kwamred Bashir Isa yace danuwansa ya rasu sanadiyar harbeshi da 'yansanda suka yi lokacin hatsaniyar. Injishi kanin nasa Adamu Isa yana aikin plumber ne kuma lokacin da aka harbeshi yana kan babur ne ya je sayan kayan aiki

Amma kakakin rundunar 'yansandan jihar ASP Tiyana Tyope cewa kawo ya zuwa lokacin da aka tambayeshi bai samu cikakken bayani daga 'yansandan dake inda lamarin ya faru ba saboda haka sai dai a jira.

Ga rahoton Zainab Babaji da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:11 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG