Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dokokin Britaniya Za Ta Kada Kuri'ar Ficewa Daga Kungiyar Tarayyar Turai


A yau Laraba ake sa ran majalisar dokokin kasar Birtania zata kada kuri’a kan ko ya Birtaniya za ta fice daga kungiyar kasashen turai, batare da amincewa da wasu ka’idojin ficewar ba.

Yarjejeniyar da ake kira “Ba dai-daito” wacce Firaminista Thersa May taki amincewa da ita, a bangare daya kuwa ‘yan majalisar kasar sun ki amincewa da yarjejeniyar da May ta cimma da sauran kasashen kungiyar ta Turai.

A jiya Talata ‘yan majalisun sun kada kuri’ar amincewa da a sake duba yarjejeniyar. "Adadin wadanda suka kada kuri’ar amincewa a hannun dama, dari biyu da arba’in da biyu (242). Wadanda suka kara kuri’ar kin amincewa a haggu dari uku da casa’in da daya (391). Saboda haka wadanda suka ki amincewa sun yi rinjaye."

Idan kuma har ‘yan majalisun suka ki amincewa daficewa Ba-dai-daito, to za’a kada kuri’a ta uku a ranar Alhamis, wanda za’a bukaci kungiyar ta kara lokaci daga ranar 29 don sake duba wasu hanyoyi da za’a bi a fice.

Tilas ne kasashen kungiyar Tarayyar Turai su amince da duk wani Karin wa’adi da za a bukata.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG