Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dinkin Duniya Za Ta Karfafa Zaman Lafiya A Afghanistan


Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, ya cimma matsaya ta bai-daya, kan a tsawaita tare da karfafa aikin wanzar da zaman lafiya a Afghanistan, matakin da ya kaucewa barazanar China ta hawa kujerar-naki.

A ranar Litinin ya kamata kwamitin ya kada kuri’a kan wannan batu, kwana guda kafin wa’adin aikin majalisar ya kawo karshe a kasar.

Sai dai China ta yi barazanar hawa-kujerar naki kan kudurin na sabunta ayyukan majalisar a kasar ta Afghanistan, saboda bai hada har da wani shirin ayyukan da ta kirkiro ba, na “samar da ababan more rayuwa kamar na samar da hanyoyin kasa da na ruwa, wadanda za su hada Chinan da nahiyoyin Asiya, Turai da Afirka.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG