Jami’an Amurka sun ce ana ci gaba da samun karin hujjojin da ke nuna cewa Iran ce da alhakin hare-haren da akai kai a kan matatun man kasar Saudi.
Da farko ‘yan tawayen Houthi na kasar Yemen da ke samun goyon bayan kasar ta Iran, sun dauki alhakin kai hare-haren na ranar Asabar, wadanda suka kassara kusan rabin ayyukan tace man kasar.
Sai dai jami’an Amurka, sun ce hujjojin da aka tattara, sun nuna cewa, ba ‘yan tawayen na Houthi ne suka kai harin ba.
A jiya Talata, wani jami’in tsaron Amurka, ya fadawa Muryar Amurka cewa, bayanan da suka tattara, sun nuna cewa Iran ce ta kitsa hare-haren.
Martin Grifiths, shi ne wakilin Sakatare-janar din Majalisar Dinkin Duniya na musamman, kan rikicin Yemen.
“Ya kara da cewar, wannan babban al’amari zai iya janyo rikici a daukacin yankin, sama da yadda zai iya samar da hanyoyin sasantawa.”
Iran dai ta musanta cewa tana da hannu a harin na Saudiyya.
Facebook Forum