Majalisar ta ce babu isassun kayan aiki don yakar annobar, kuma lamarin zai kara ta'azzara yayin da lokaci ya tafi. Majalisar Dinkin Duniyar ta na neman dala miliyan 640 don yakar cutar, kuma ta yi gargadin za a iya fuskantar babbar matsala idan ba a dauki matakin gaggawa ba.
Majalisar Dinkin Duniya Ta Yi Gargadin Cewa Mutane Biliyan Daya A Kasashe 43 Na Fuskantar Barazanar Kamuwa Da Cutar Kwalara