Directan shirin cutar HIV na majalisar dinkin duniya, Michel Sidibe, ya bayyana tabbacin goyon bayan kauda cutar HIV tsakanin masu shan kwayoyi. Yayi wannan bayani ne lokacin da yake marabtar sabon binciken magungunan kare cutar HIV.
Sabon binciken ya nuna cewa shan maganin kare HIV kowacce rana, zai iya rage hatsarin cutar HIV da kusan rabi, a cikin masu cutar maza da mata dake yiwa kansu allurar maganin. Kuma amfani da wannan maganin kare cutar sida yana da inganci wajen kare mutane masu cutar da kuma hana wadansu kamuwa da ita.
Mr Sidibe, ya kara da cewa UNAIDS basu yarda da hanya daya kawai ta kariyar yaduwar cutar HIV ba, da kuma hadi da kiyaye kayan aiki kamarsu allurai da sauran kayan asibiti.
Kayan aikin lafiya tare da kauda dokoki marasa karfi da kuma hadin kai da ‘yan sanda da wadansu hanyoyin inganta dokoki, sun taimaka wajen hana yada cutar HIV tsakanin mutane masu yiwa kansu allurar maganin.
Wani sabon binciken da ma’aikatar lafiya ta Amurka ta gudanar, ya gano cewa maza da matan da suka sha allurar maganin ta baki, suna kamar kashi 49% kasan wadanda zasu iya kamuwa da cutar HIV.