Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dinkin Duniya Ta Shiga Tsakanin Rikicin Yamal


Wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman Ismail Ould Cheikh Ahmed ya bude taron shiga tsakani a rikicin kasar Yemen
Wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman Ismail Ould Cheikh Ahmed ya bude taron shiga tsakani a rikicin kasar Yemen

Majalisar Dinkin Duniya ta yi nasarar shiga tsakani a kokarin kawo karshen yakin kasar Yamal, amma kuma ba tare da samun cikakkiyar hanyar yadda za a kawo karshen rikicin ba.

Bayan taron da aka yi a Geneva, Wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman, Isma’il Ould Sheikh Ahmed, ya bayannna cewa jami’an gwamnatin kasar da aka amince da ita, da bangaren ‘yan tawayen Houthi, za su sake zama a wata mai zuwa.

Ya kuma gayawa manema labarai cewa, har yanzu ana ci gaba da fada da kuma kai hare-hare, yayin da bangarorin biyu suka kasa cimma wata kwakwarar matsaya.

Ahmed ya ce, duk cewa an kasa aiwatar da shirin tsagaita wuta da bangarorin biyu suka amince a baya, za su yi kokari suga an kulla wata sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta nan da ‘yan kwanaki masu zuwa.

Jami’an kasar ta Yamal sun ce fadan da aka yi a kwanan nan a Lardin Hajja da ke kusa da iyakar Saudiyya, ya halaka mutane 68.

Ministan harkokin wajen kasar, Abdel Malak- al Mekhlafi, ya ce za su yi kokarin sabunta shirin tsagaita wutar, wanda zai kawo karshe a yau Litinin, idan har ‘yan tawayen Houthi suka mutunta yarjejeniyar.

A dai watan Satumban 2014 rikicin na Yamal ya barke a lokacin da ‘yan tawayen Houthi suka karbe ikon Sana’a, babban birnin kasar, lamarin da ya tilastawa shugaban kasar Abdu Rabu Mansour Hadi yin kaura zuwa birnin Aden inda ya dangana har zuwa Saudiya.

XS
SM
MD
LG