Shugaban hukumar sa idanu kan harkokin nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya (IAEA) ya yi kira ga gwamnatin Trump da kasar Iran su tattauna da juna, sakamakon hanzarta samar da tataccen makamashin uranium da mahukuntan birnin Tehran ke yi.
Babban daraktan IAEA, Rafeal Grossi, ya ce hawa kan teburi “na da matukar muhimmanci” domin samun ci gaba a tattaunawar da ake yi da mahukunta birnin Tehran.
“Matukar ba’a tattauna ba, babu wani ci gaba da za a samu,” kamar yadda Grossi ya bayyana wa manema labarai a taron kolin tattalin arzikin duniya da ke gudana a birnin Davos, na kasar Switzerland.
Kalaman Shugaba Donald Trump da mambobin sabuwar gwamnatinsa na nuna cewa “akwai alamun za a iya hawa kan teburin tattaunawa watakila ma a samu kulla yarjejeniya”, a cewar Grossi.
Suma jami’an kasar Iran sun amince da cewar akwai bukatar tattaunawar, kamar yadda yace.
Shirin nukiliyar Iran ya bunkasa cikin sauri a fannin kwarewa da gine-gine da jerin kayayyakin hada makamin nukiliyar tun karshen wa’adin mulkin Trump na baya a 2021, a cewar Grossi.
A zamanin wa’adinsa na farko, Trump ya yi amfani da manufar yin matsin lamba mai tsanani a kan Iran, inda ya janye Amurka daga shahararriyar yarjejeniyar nukiliyar nan ta 2015 wacce ta kakaba takunkumi a kan shirin nukiliyar Iran domin sassauta mata takunkuman.
Dandalin Mu Tattauna