Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

MDD: Yau ce Ranar Bada Agaji ta Duniya


Mutane na karban kayan agaji
Mutane na karban kayan agaji

Majalisar Dinkin Duniya ta kebe 19 ga watan Augusta na kowace shekara a matsayin ranar da ake tara agaji domin kulawa da wadanda bala'i ka iya addaba a koina a duniya.

A kasashen Najeriya da Nijar mutane sun sha fama da bala'o'i iri-iri.

Shekaru da dama ke nan da arewacin Najeriya musamman arewa maso gabas ke fama da ta'adancin da Boko Haram ke haddasawa. Mutane da yawa sun rasa rayukansu. Wasu masu dimbin yawa sun jikata sun kuma rasa muhallansu. Akwai wadanda suka tagayyara. Wasu sun kidime saboda abubuwan da suka gani da muguwar azaba da suka sha.

Ambaliyar ruwa a wurare daban daban da gobara da rikicin addini ko na kabilanci duk sun haddasa mugun bala'i. An yi kashe-kashe da kone-kone. Akwai yaran da yake an rabasu da iyayensu har abada.

Saboda shirin ko ta kwana kungiyoyin jin kai da masu tallafawa jama'a ya sa suna neman taimako daga kowa suna tarawa domin kawo taimako yayinda ake bukata. A Najeriya akwai kungiyoyi da dama da suke fadakar da jama'a mahimmancin bada tallafi idan aka bukacesu su yi hakan.

Yau a Jamhuriyar Nijar kungiyoyin bada agaji zasu taru su kawo fadakarwa akan wannan ranar. Rana ce kuma ta tunawa da wadanda suka sadakar da kansu domin su kawowa wasu agaji.

Misali a jihar Maradi akwai gungiyoyi da dama da suke kawo agaji musamman ga wadanda rikicin Boko Haram ya rutsa dasu da ambaliyar ruwa da kuma rikicin kabilanci.

Aikin agaji na fuskantar wasu matsloli.Na farko mutane sukan sa son rai. Idan wasu sun shiga wata matsala aka kawo masu agaji sai wadanda basa cikin wata damuwa su ce dole su ma a tallafa masu. Wasu kuma na ganin masu hannu da shuni ne kawai ya kamata su bada agaji. Lamarin ba haka yake ba. Taro da kwabo idan ana tarasu zasu kai yadda zasu iya taimakawa. Wato haki ne akan kowa ya bada agaji komi kankancinsa.

Agaji kala kala ne. Ana iya bada agajin kudi ko magani ko abinci ko kuma kayan gini. Haka ma akwai agajin kayan kwanciya ko rumfunan kwana.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:06:40 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG