Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnati da 'Yan Tawayen Sudan ta Kudu Na Taron Sulhu a Habasha


Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir
Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir

Shugabannin kasashen yankin gabashin Afirka suna bukatan gwamnatin Sudan ta Kudu da 'yan tawaye sun cimma daidaito yau akan wanzar da zaman lafiya

A yau Litinin Shugabanni daga yankin gabashin Afrika na yunkurin su ga cewa gwamnatin Sudan ta Kudu da ‘yan tawayen kasar, sun saka hanNu a shirin samar da zaman lafiya, domin kawo karshen yakin basasan da aka kwashe watannin 20 ana yi a kasar.

Shugaba Salva Kiir da abokin hamayyrasa Riek Machar, suna halartan zaman da ake yi yanzu haka a Addis Ababa, wanda ke samun jagorancin kungiyar kasashen gabashin Afrika ta IGAD.

Shugaban Kenya, Uhuru Kenyatta, ya saka hotunanan Shugaba Kiir da Machar a shafinsa na Twitter, yayin da suke halartar taron a jiya Lahadi.

Hakan na faruwa ne yayin da ake kokarin a kaucewa cikar wa’adin da aka shata na yau Litinin ba tare da an samu matsaya kan yadda za'a kawo karshen rikicin ba.

Wannan zaman tattaunawa dai na gudana ne hade da goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya.

Shugaba Kiir ya halarci taron ne, kwanaki biyu bayan da ya ayyana cewa ba zai je kasar ta Habasha ba saboda a cewar shi, ‘Yan tawayen sun rabu zuwa gida biyu.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG