A yayin da Yarima Harry da mai dakinsa suka iso Najeriya, ana sa ran za su ziyarci biranen Abuja da Kaduna da kuma Legas, kamar yadda Kakakin hedkwatar tsaron kasar Birgediya Janar Tukur Gusau ya sanar.
Ziyarar ta Harry na kwana uku domin halartar bukukuwan cika shekara 10 da kadamar da wasannin 'Invictus Games' na sojojin da aka raunata a fagen daga.
Gasar ta motsa jiki ce na sojoji da suka raunata a wurin yaki.
Janar Gusau ya ce shi kansa Yariman shi ma tsohon soja ne, don haka ya san me ake nufi da in aka ce soja ya sami rauni a fagen daga.
Bugu da kari ita ma mai dakinsa, Gimbiya Meghan wacce bakar fatar Amurka ce, ta sa an mata wani bincike da ya nuna asalin kakanninta daga Najeriya su ke.
Daga bisani dai Yariman zai je jihar Kaduna inda zai gana da nakassun sojojin da suka sami rauni kuma suke jinya a asibitin sojoji na 44 REFFERAL da ke Kadunan kuma zai gana da Gwamnan jihar.
Daga nan kuma zai koma Abuja inda za a dan shirya musu liyafar cin abinci, ya kuma wuce jihar Legas idan ya dawo kuma zai koma gida Birtaniya.
Yarima Harry wanda da ne ga Sarki Charles na uku da Gimbiya Diana, tsohon soja ne da ya fafata har sau biyu a karo daban-daban a yakin Afghanistan, kuma mutum na biyar cikin jerin masu jiran gadon sarautar Birtaniya.
Bayan ya bar aikin soji, ya kirkiro da gasar wasannin motsa jiki a matakin kasa da kasa na sojojin da suka sami nakasa a fagen daga mai suna INVICTUS GAMES.
Masana tsaro irin su Wing commander Musa Isa Salman mai ritaya na ganin wannan ziyara na da muhimmanci sosai musamman kasancewarsa tsohon soja kuma ‘dan sarauta mai kwarjini da farin jini.
Dandalin Mu Tattauna