Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu ‘Yan Bindiga Sun Sace Dalibai A Jami’ar Jihar Kogi


'Yan bindiga
'Yan bindiga

A ranar Alhamis da daddare ne ‘yan bindiga suka mamaye Jami’ar Kimiyya da Fasaha (CUSTECH) dake yankin Osara, a Jihar Kogi, inda suka yi awon gaba da wasu dalibai.

A cewar wasu kafofin watsa labarai na cikin gida, ‘yan bindigar sun kai farmaki jami’ar ne da misalin karfe 9:00 na dare, yayin da dalibai da ke cikin aji suna shirye-shiryen zana jarbawa a Jami'ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kogi (CUSTECH), inda suka dauke dalibai da kawo yanzu ba a tantance adadinsu ba.

Rahotanni daga jami’ar sun ce, lokacin da jami’an tsaron jami’ar suka kawo dauki, tuni ‘yan bindigar sun yi nasarar awon gaba da wasu daliban.

Zuwa wannan lokaci dai babu cikakken bayani daga jami’an tsaro.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG