Ana saran za'a tanatance takwas daga cikin mutanen cikin wannan mako. Za'a fara ne da dan majalisar dattijai na jam'iyar Republican Jeff Session, wanda Trump ya dauka ya zama Atoni Janar kuma ministan shari'a.
Wasu 'yan jam'iyyar Republican sun ce lokacinda shugaba Obama ya kama aiki a 2009,an amince da mutane da ya zaba a zaman farko. Senata John Barrasso ya gayawa Muryar Amurka cewa, suna fata za'a sakawa kura anniyarta.
Amma 'yan Democrat suna korafin cewa da yawa daga cikin wadanda Trump ya zaba suna sanyin jiki wajen cike ko bada bayanai da ake bukata daga duk wadnda aka baiwa irin wadannan mukamai.
Da yake magana shima kan ministocin da ya zaba, shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump yace, yana da kwarin gwuiwa duk zasu sami amincewa.