Jiya litinin Trump ya aike da sako ta shafinsa na twitter yana mai cewa “ba zata sabu ba”.
Trump kuma ya sake caccakar kasar china kamar yadda ya taba yi a baya akan gazawa wajen hana kasar Koriya ta arewa dake kawaye, shirin kirkiro makami mai linzami da kuma na nukiliya.
Trump ya ce China ta sha karbar makudan kudade da dukiyoyi daga Amurka ta fannin kasuwancin da ta fi karuwa da shi, amma ta ki taimakawa akan Koriya ta arewa.
Koriya ta kudu ta yaba da sakonnin twittern Trump kan yadda ya nuna cikakkiyar fahimtarsa kan hadari da kuma irin barazanar da shirin nukiliyan Korea ta arewa ke tattare da shi.