A yau Litinin China ta nuna adawarta da kan duk wata hulda tsakanin shugaban Taiwan da hukumomin Amurka, kwana daya bayan da shugabar ta Taiwan Tsai Ing-wen ta hadu da Sanata Ted Cruz da kuma gwamnan jihar Texas Geg Abbot.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen China, Lu Kang, ya fadawa manema labarai cewa, China ba ta amince da duk wata hulda da ta ke barazana dangantakar China da Amurka ba.
A wannan ganawa da shugabannin bangarorin biyu suka yi, ta auku ne a Houston inda shugabar ta Taiwan ta yada zango a birnin na Houston yayin da ta ke kan hanyarta ta zuwa Tsakiyar yankin Amurka.
Sanata Ted Cruz ya ce maksudin wannan zama da suka yi ya, ya ta’allaka ne kan batutuwa harkokin kasuwanci da kuma yadda za a taimakawa manoma da makiyaya da kuma tallafawa masu kananan sana’oi.
A kwanakin baya shugaban Amurka mai jiran gado, Donald Trump ya sha suka bayan da ya yi magana ada shugabar ta Taiwan ta wayar talho, jim kadan bayan da ya lashe zaben kasar.