Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dakatar Da Sanata Ningi Zai Hana Wasu 'Yan Majalisa Bayyana Ra'ayinsu – CISLAC


Abdul Ningi
Abdul Ningi

Matasan Arewa da wata kungiyar kare 'yancin fararen hula da dimokradiya CISLAC, sun nuna cewa dakatar da Sanata Abdul Ningi a Majalisar Dattawa, dakile 'yancin fadin albarkacin baki ne.

Kungiyar kare 'yancin fararen hula da dimokradiyya CISLAC ta zayyana dakatar da Sanata Abdul Ahmed Ningi mai wakiltan Bauchi ta Tsakiya a majalisar dattawa da matakin da ya yi karantsaye ga tsarin mulki.

SENATOR ABDULAZIZ 'YAR'ADUA
SENATOR ABDULAZIZ 'YAR'ADUA

A sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban CISLAC Auwal Musa Rafsanjani, kungiyar ta nuna fargabar dakatar da Abdul Ningi zai hana wasu 'yan Majalisa bayyana ra'ayin su, ko fitar da bayanai don gano gaskiyar lamura.


A hirar shi da Muryar Amurka, mai sharhi kan lamuran yau da kullum Muhammad Shu'aibu Bakwai ya ce matakin Majalisar dattawan abun mamaki ne yayin da sabuwar dimokradiyyar Najeriya ke cika shekaru 25.

Auwal Musa Rafsanjani
Auwal Musa Rafsanjani


Shi kuma kakakin Majalisar Matasan Arewa Ambasada Abdul Dan Bature ya bukaci Majalisar dattawan ta janye dakatarwar inda ya yi bayani cewa su na son shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio da Majalisar baki daya su gaggauta janye dakatarwar da su ka yi ma shi.

Abdul ya ce suna son Majalisa ta yi masu bayani kan cushen kudi Naira triliyan 3.7 da Ningi ya ce an yi a kasafin kudin bana. Abdul ya ce su matasa ba za su yarda da irin wannan mataki da Majalisar ta dauka ba domin zai zama kamar ana so a hana wasu dattawa fadin albarkacin bakin su ne, kuma wannan ya saba wa kundin tsarin mulkin kasa.

Ita ma Shugabar wata kungiyar gyara tarbiyyar matasa Halima Baba Ahmed ta yi tsokaci cewa, abun da Sanata Ningi ya yi abun yabo ne a yayin da a ke kara zargin Majalisar dokokin da zama 'yar amshin shatan fadar Shugaban kasa, Aso Rock.

Tuni Kungiyar Sanatocin Arewa ta nada Sanata Abdulaziz 'Yar'adua ya maye gurbin Abdul Ningi a shugabancin Kungiyar, kuma ya yi wa Muryar Amurka bayani cewa zai rika tuntubar Ningi don kwarewar sa.

Tun bayyanar kalaman Sanata Ningi na samun kasafi kala biyu, mai baiwa shugaba Tinubu shawara kan sadarwa Bayo Onanuga ya nuna takaicin cewa kalaman sun fito daga babban dan majalisa.

Majalisar dattawa ta dakatar da Ningi na tsawon watanni 3 don zargin rufa-rufa ko cushe da ya ce an yi a kasafin kudin Najeriya na bana.

Saurari rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:16 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG