Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dattawa Ta Kira Buhari Ya Sake Gabatar Mata da Bukatarsa Ta Ciwo Bashi


Sanata Dr. Aliyu Sabi Abdullahi, kakakin Majalisar Dattawa
Sanata Dr. Aliyu Sabi Abdullahi, kakakin Majalisar Dattawa

Majalisar Dattawan Najeriya ta amincewa shugaban Najerya da ya sake mika kokon baran neman ciwo bashin dalar Amurka biliya talatin daga kasashen waje

Sai dai tun daga lokacin da shugaban Majalisar Dattawan Abubakar Bukola Saraki yace wa shugaban kasa Muhammad Buhari ya sake dawowa majalisar da bukatar ciwo bashin dala biliyan talatin ne a ke ta sukan gwamnati.

Wasu 'yan majalisar na matukar bukatan a sake tsarin da Shugaba Buhari ya shimfida na ciwo bashin. Wasu ma na neman a yi watsi da al'amarin gaba daya saboda acewarsu, Najeriya tumbin giwa ce.

Mai magana da yawun majalisar dattawan Dr Aliyu Sabi Abdullahi yace majalisar ce tace a dawo da bukatar ba shugaban majalisar ba. Yace majalisar ta sake nazari. Shugaban kasa yana da adalci to amma ba shi ba ne zai yi ayyukan ba. Mutane ne zasu yi ayyukan. Yace idan mutanen da zasu yi ayyukan basu tantance masu abubuwan da zasu yi ba to babu tabbas inda a ke.

Yace sun amince a ranci kudi saboda akwai shi a kasafin kudin shekarar nan, rancen kudi ciki da wajen kasar.

Onarebul Jagaba Adams Jagaba, wanda yake goyoon bayan a ciwo bashin
Onarebul Jagaba Adams Jagaba, wanda yake goyoon bayan a ciwo bashin

Shi kuwa dan majalisar wakilai Jagaba Adams Jagaba cewa yayi tunda ba asusun gwamnati kudaden zasu shiga ba yayi na'am da ciwo bashin. Yace idan dan kwangila yayi aiki bankin duniya ne zai biya kai tsaye. Inji shi tunda yake ba'a taba cin bashin da zai yiwa mutane anfani ba kamar wannan ba.

Ga rahoton Medina Dauda da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:30 0:00

XS
SM
MD
LG