Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Najeriya Ta Gudanar Da Taro Game Da Shirin Tallafawa Jama’a


Yemi Oshinbajo
Yemi Oshinbajo

A Jahar Kano mataimakin shugaban kasar Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo, ya jagorancin zauren ganawa da kungiyoyin ‘yan Kasuwa da masu sana’o’i game da shirin tallafawa Jama’a su dogara da kansu na gwamnatin tarayya.

Shirin wanda ya kunshi tsarin N-Power na samarwa matasa aikin yi da kuma tsarin agazawa iyalan dake fama da talauci a cikin al’umma wajen karatun ‘ya ‘yansu da kuma tallafawa masu sana’o’i da kananan ‘yan kasuwa, ma’aikatar mata ta tarayya da hadin gwiwa da ofishin mai baiwa shugaban kasa shawara kan lamuran tallafawa jama’a ne zasu aiwatar da shi.

A cewar Hajiya Maryam Uwais mai baiwa shugaba Buhari shawara kan lamuran tallafawa jama’a domin dogaro da kai, gwamnatin tarayya zata bayar da bashi daga dubu 10 zuwa 100 wanda babu kudin ruwa ciki ga matasa da mata da manoma da masu kananan sana’o’i.

Haka kuma akwai wani tsari ga matasan da suka sami shiga jam’o’i domin koyon darussan da suka hada da: kimiyya da fasaha da Injiya da kuma lissafi, kowanne wata za a taimaka musu da kudi Naira Dubu 45.

Wannan dai shine karo na biyu da mukarraban gwamnatin tarayya ke gabatar da irin wannan taro cikin watanni uku zuwa hudu, kuma wannan taro yazo dai dai da lokacin da Kanawa ke ci gaba da korafin cewa gwamnatin Najeriya ta mayar da su saniyar ware a shirin samar da aikin yi na N-Power.

Kafin mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya kai rangadin duba kamfanin sarrafa Tumatir na Dangote dake kan titin zuwa Zaria daga Kano.

Domin karin bayani saurari rahotan Mahmud Ibrahim Kwari.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:33 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG