Mai yiwuwa takaddamar dake tsakanin fadar shugaban kasa Muhammad Buhari da shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ta haifar da wannan jinkirin tabbarawa Ibrahim Magu shugabancin hukumar EFCC.
Har yanzu dai ita hukumar EFCC tana cigaba da tuhumar shugaban majalisar dattawan da rashin ambata kaddarorinsa tun yana gwamnan jihar Kwara gaban kotun da'a ta ma'aikata.
Duk da cewa gwamnatin Buhari yta janye tuhumar shi Bukola Sarakin da sauran shugabannin majalisar dattawan akan zargin sun yi anfani da dokar bagi wajen darewa mukaman majalisar.
Dr Sadiq Umar Abubakar Gombe mai sharhi akan lamuran siyasa yana da ra'ayin rade-radin da a keyi akan takaddamar dake tsakanin fadar shugaban kasa da ofishin shugaban majalisar dattawa. Yace an yi maganganu masu dama kuma har yanzu suna ta yawo ba tare da samarda wata masalaha da zata sa a san inda aka dosa ba. Yace yana ganin wasu suna son su nuna sun fi karfin doka ko a matsayinsu na 'yan jam'iyya ko kuma a wani matsayi daban.
Inji Dr Gombe haka suka yi a lokacin Ibrahim Lamorde akan abubuwan da basu taka kara sun karya ba. Sai da suka ga an fitar dashi. Shugaban kasa ya kawo Ibrahim Magu kuma ya zo yayi aiki amma kuma ba'a son a tabbatar dashi saboda suna tunanen makomarsu idan sun tabbatar dashi a yaki da cin hanc da rashawa a karkashin shi Magu.
Wani masanin shari'a Barrister Kogo Ibrahim yace kamata yayi majalisa ta dubi bukatun kasa da doka wajen tantance Ibrahim Magun. Yace dole ne a yi la'akari da bukatun kasa. Bangarorin dokokin kasar duk sun kira a sanya kasa gaba ba son rai ba.Kowane bangaren gwamnati yayi tunanen kishin kasa. Acewarsa Ibrahim Magu ya nuna yana iya aikin cikin lokacin da yake rikon kwaraya. Yakamata a tabbatar masa da mukamin domin akwai wasu abubuwan da ba zai iya daukan mataki a kansu ba a matsayinsa na shugaban riko.
Shugaban kwamitin labaru na majalisar dattawan Dr. Aliyu Sabi Abdullahi yayi bayani a madadin majalisar. Yace zargin da ake yi masu bashi da tushe. Yace ba'a tabbatar da mukami mai mahimmanci irin na hukumar EFCC sai an tabbatar an samu 'yan majalisa fiye da kashi saba'in a zauren taronsu saboda gudun kada wani ya ce inda yana majalisa da bai yadda da abun da majalisar tayi ba.
Ga rahoton Medina Dauda da karin bayani.