Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisa Ta Yi Watsi Da Kasafin Kudin Ma'aikatar Yada Labaran Najeriya


Ministan yada labarai, Mohammed Idris (Hoto: Facebook/Ministry of Information)
Ministan yada labarai, Mohammed Idris (Hoto: Facebook/Ministry of Information)

Majalisar dokokin Najeriya ta yi watsi da kasafin kudin Ma'aikatar yada labarai da wayar da kan al'umma ta kasa da dukkan hukumomin da ke karkashin ma'aikatar.

Majalisa ta ce minista ya koma yaje ya kawo wani kasafin, kuma wannan shi ne karo na biyu da haka zai faru, domin ko a shekarar 2024 ma haka aka yi watsi da kasafin ta.

Mataimakin shugaban kwamitin kula da ma'aikatar yada labarai da wayar da kan al'umma, Sanata Garba Musa Maidoki, ya shaida wa Muryar Amurka cewa, majalisa ta ki amincewa da kasafin kudin ma'aikatar yada labaran a karo na biyu, domin kasafin da ma'aikatar ke kawowa ba zai wadatar da ma'aikatar da hukumomin da ke karkashin ma'aikatar wajen gudanar da ayyukan su yadda ya kamata ba.

Maidoki ya ce daga dukan alamu rashin isassun kudi da kayan aiki suna sawa a samun karancin fahimtar manufofin gwamnati da yadda ya kamata a hada kan kasa domin a samu zaman lafiya.

“Ko ba komai ya kamata ma'aikatar ta kawo kasafi daga Naira biliyan 250 ko fiye da haka, inda ya ba da misali da kasar Afirka ta Kudu da ke da mutum miliyan 50, wato kashi daya cikin hudu na yawan mutanen Najeriya kusan miliyan 250, amma tana ware Naira biliyan 450 wa ma'aikatar yada labaran ta,” in ji Maidoki.

Shi kuwa tsohon ma'aikaci da ya kwashe shekaru 32 yana aiki a gidan Radiyon Tarraya Najeriya, Abdullahi Umar Kwarbai, ya ce lallai biri ya yi kama da mutum, domin a lokacin da ya ke aiki ana samun koma baya sosai, domin babu kayan aiki na zamani da zai taimaka wajen gudanar da ayyukan yada labarai kamar yadda ya kamata.

Kwarbai ya ce ana samu lokuta da dama da gidajen radiyo da mutane ke dogaro da su wajen samu labarai, ba sa aiki.

Da yake tsokaci, wani ma'aikaci a gidan talebijin mai zaman kansa, Mallam Sadiq Nuhu Sabon Wuse, ya ce abin da ya kamata shi ne majalisa da bangaren gwamnati su hada kai su yi aiki tare wajen kawo wa ma'aikatar yadda labarai mafita, domin kuwa tana cikin wani mawuyacin hali.

Majalisa ta ba Ministan Ma'aikatar Yada labarai Mohammed Idris Malagi mako daya ya sake kawo wani sabon kasafin kudin da ma'aikatar za ta yi aiki da shi a wannan shekara.

Saurari cikakken rahoton Medina Dauda:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:14 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG