Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mai Yiwuwa Rauni Ya Hana Rodrygo Buga Wasan ‘El Clasico’


Rodrygo (Photo by Pierre-Philippe M
Rodrygo (Photo by Pierre-Philippe M

Ana sa ran dan wasan gaban na Madrid wanda dan asalin kasar Brazil ne zai yi wasu gwaje-gwaje kafin wasan gida na ranar Asabar.

Akwai yiwuwar dan wasan gaba na Real Madrid, Rodrygo, ba zai buga wasan “el clasico” da za su yi da Barcelona a ranar Asabar ba bayan ya fice daga wasan Gasar Zakarun Turai na ranar Talata saboda raunin da ya ji.

Rodrygo ya bar filin wasa a minti na 85 kuma Aurélien Tchouaméni ya maye gurbinsa a wasan da Real Madrid ta yi nasara da ci 5-2 bayan da aka fara zura mata kwallo biyu a hannun Borussia Dortmund a filin wasa na Santiago Bernabeu.

Kocin Madrid, Carlo Ancelotti, ya ce ba zai yi wu Rodrygo ya buga wasan da Barcelona ba.

Ana sa ran dan wasan gaban na Madrid wanda dan asalin kasar Brazil ne zai yi wasu gwaje-gwaje kafin wasan gida na ranar Asabar.

Vinicius Junior ya zura kwallaye uku a raga yayin da Real Madrid ta canza kukanta zuwa murna da nasarar 5-2 a kan Borussia Dortmund ta kasar Jamus.

Dandalin Mu Tattauna

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG