Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mai Ba Trump Shawara Ta Ba Da Shaida A Majalisar Wakilan Amurka


Tsohuwar mai baiwa shugaban Amurka Donald Trump shawara kan Rasha da yankin Turai, Fiona Hill, ta ba da shaida a sirrince, a binciken da ke duba yiwuwar tsige shugaban, inda mai yiwuwa ta yi karin haske ne kan sallamar da Trump ya yi wa tsohuwar jakadar Amurka a Ukraine a watan Mayu wato Marie Yovanovitch.

A makon da ya gabata, Yovanovitch, wacce jami’ar diflomasiya ce a ma’aikatar harkokin wajen Amurka, ta fada wa ‘yan majalisa cewa Trump ya kore ta ne sakamakon wasu zarge zarge “marasa tushe da karerayi” da aka yada akanta, bayan da lauyan Trump, wato tsohon magajin garin New York, Rudy Giuliani, ya nuna bai gamsu da aikinta da take yi a birnin Kyiv ba.

Shi dai Giuliani ya nemi Ukraine ta binciki daya daga cikin manyan masu hamayyar siyasa da Trump, wato tsohon Mataimakin Shugaban kasar Joe Biden, da rawar da ya taka a shekarun baya a lokacin da aka kori mai gabatar da kara na kasar ta Ukraine.

Ya kuma nemi a binciki zamanin da Hunter Biden mai shekaru 49 ya samu alheri, a lokacin yana mamba a kwamitin amintattun wani kamfanin Ukraine na samar da makamashi mai suna Burisma.

Shi dai Biden da dansa sun musanta aikata ba daidai ba, kuma watanni da dama da suka gabata, shi Hunter ya bar kamfanin na Burisma.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG