Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu ‘Yan Niger Sun Yaba Da Zaben Wasu Kuma Suna Suka


Niger election banner
Niger election banner

Wakilin sahen Hausa daga Maradi Shaibu Mani ya jiwo daga bakin wasu masu jefa kuria kuma wasun su sun yaba wasu kuma sun soki zaben.

Da farko Shaibun ya tattauna da Sule Abdu mna jamiyyar PNDS tarayya yake cewa.

‘’Alhamdulillahi zabe kamar irin yadda muke fata ALLAH ya taimaka haka nan yake wakana a wurare daban-daban inda runfunar zaben suke kuma munga kamar yadda akayi wannxcan na farko haka yake nan yana wakana, wato mutane sun fara fitowa sosai domin su sauke nauyin zabe na shugaban kasa zagaye na biyu.’’

Sai dai da Shaibu yace masa to sai dai wannan karon ‘yan adawa sun kaurace wa zaben kome zai ce, sai ya amsa da cewa.

Ba shakka ‘yan adawa sun kauracewa zaben, kamar yadda mutane suka sani shine demokadiyya tunda ko suna da damar suyi hakan duk da yake ba haka aka so ba don kara wa abin armashi ina ganin babu wata damuwa.’’

Sai dai har wayau Shaibun yace masa to mutun na iya kouwa shi kadai, anan ko sai ya amsa da cewa idan bai samu abokin karawa ba sai ya shiga fage yayi kirari..

Sai dai a bangaren lumana kuma Amadu Mammam Dutse ya shaidawa Shaibu cewa.

‘’Mu gare mu ba wannan zabe mun kira wakilan mu na cikin hukumar zabe wato CENI na kasa gaba daya dana jiha duk mun fidda su, haka ma runfunar zabe suma mun fidda su.

Don haka muna kira cewa duk wanda yatafi wannan zabe ba yawun ‘yan adawa ba, bada yawun dan takara ba Hamma Amadu ba.’’

Ga Shaibu Mani da cin gaban hirar da sauran mutane 3'31

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:15 0:00

XS
SM
MD
LG