Taron ya samu halartar mutane fiye da dubu goma wadanda suka lashi takobin cewa yanzu a shirye suke su sadakar da rayuwarsu su farauto 'yan kungiyar Boko Haram domin kawo karshen hare-haren dake neman kassara jihar baki daya.
An kwashe kusan sao'i hudu ana taron tare da yin jawabai a filin sukuwa dake birnin Maiduguri. Bayan sun gama taron sun wuce fadar mai martaba Shehun Borno domin neman tabarraki da kuma bayyana masa irin nufin da suke dashi.
Wakilin Muryar Amurka ya halarci taron. Ya zanta da Alhaji Abba Kalli shugaban shirya taron akan makasudin taron. Yace sun gayyaci jami'an tsaro 'yan aslin jihar Borno da suka yi ritaya domin su shaida masu halin da ake ciki. Yace su sun sadakar da rayuwarsu domin su ceto jiharsu daga ta'adancin 'yan Boko Haram. Yace basa tsoronsu ko kadan.
'Yan kungiyar kato gora ko Civilian JTF sun ce babu yadda zasu juyawa 'yan Boko Haram baya. Suna jira ne a basu dama su fita su shiga dajin Sambisa inda 'yan Boko Haram suka yi kakagida.
Su ma kungiyar maharba da suka halarci taron sun ce sun zo ne su roki gwamnati ta taimaka domin su yaki 'yan Boko Haram. Idan sun yaki Boko Haram su ne suka yi jihadi domin 'yan Boko Haram sun manta da Allah. Mutumin da zai kashe uwarsa da ubansa ya manta da Allah. Idan gwamnati ta bada hadin kai ashirye suke su farauto 'yan Boko Haram.
A fadar Shehun Borno, mai martaba Alhaji Umar Garbai El-Kanemi ya jawo hankulan mahalarta taron akan mahimmancin bin doka. Su bi abun da soja ko 'yansanda suka gaya masu. Duk abun da zasu yi su bi shugabansu. Kada su tada hankali ko wata hayaniya. Kada su ji jita-jita da maganganun banza. Yace su yi sadaka da azumi.
Ga rahoton Haruna Dauda Biu.