Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mahara Sun Kashe Mai Garin Karal Jihar Taraba


Wuraren da hare-hare ya shafa a harin da 'yan bindiga suka kai a Adamawa, Fabrairu 4, 2014
Wuraren da hare-hare ya shafa a harin da 'yan bindiga suka kai a Adamawa, Fabrairu 4, 2014

Wasu mahara sun kai wani sabon hari a garin Kacalla dake jihar Taraba inda aka samu asarar rayuka,ciki har da na mai garin

Rahotanni na cewa wasu mahara ne dauke da muggan makamai suka farma garin Karal dake cikin karamar hukumar Gassol,a tsakiyan dare inda aka samu asarar rayuka ciki har da na mai garin Mallam Kachalla da kuma wata makaranta.

Yanzu haka wadannan mahara sun maida wannan baiwar Allah shiga takaba da halin ni yasu ita da yayanta.

Rundunan yan sandan jihar Taraban ta bakin kakakinta ASP David Misal ta tabbatar da wannan hari ,inda tace sama da rayuka shida suka salwanta baya ga wadanda aka raunta, to amma kuma ta sha alwashin zakulo maharan.

Cikin kwanakin nan dai ana samun irin wadannan hare haren a wasu sassan jihar Taraban dake da yawan kabilu,batun da kullum hukumomin tsaro ke cewa suna nasu kokari, to amma kuma suma jama’a an shawarce su da suke sa ido,kamar yadda kakakin yan sandan ke karin haske.

Saurari Cikakken rahoton Ibrahim Abdul'aziz.

Rahoton Harin da aka kashe mai garin Kacalla-3:25"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:43 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG